Nov 8, 2025
Daga LOIS DADUUT & CHRISTY ZI

Gwamnatin Filato ta ƙara ƙarfafa taimaka wa matasa ta fannin ƙirƙire-ƙirƙire a fannin yawon bude ido da kasuwanci.
An gudanar da wannan shiri ne ta hanyar Plateau Youth Tourism Roundtable da Ma’aikatar Yawon Bude Ido, Al’adu da Masaukin Baki ta shirya a cibiyar Usuji Event Centre dake Jos.
Taron ya nufi hada matasa wajen tsara makomar harkar yawon bude ido ta jihar, tare da mayar da hankali kan dorewa, kirkire-kirkire, da hadin gwiwar tsararraki.
Da yake jawabi, Kwamishinan yawon bude ido, Cornelius Doeyok, ya bayyana cewa gwamnatin Mutfwang tana aiki tuƙuru wajen samar da damar da matasa za su bunƙasa basirarsu su da kuma bayar da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin jihar.
Kwamishinan ya jaddada cewa makomar tattalin arzikin jihar na da nasaba da fannin yawon buɗe ido, saboda haka gwamnati ke taimaka wa matasa wajen gano damar da ke tattare da wannan fanni.
“Ƙirƙirar hanyoyin yawon buɗe ido ba wai gina abubuwan tarihi kawai ba ne; yana nufin ƙirƙirar sabbin hanyoyi na tattaunawa, labarai ta hanyar yanar gizo ko intanet da kuma nuna assalin yanayin jama’ar jihar,” in ji Doeyok.
Kwamishinan ya yi kira da a mai da hankali kan ɗorewar kula da muhalli, da kuma sanya irin kayayyakin da ake nomawa a jihar cikin harkar kayayyakin bajewa ga masu yawon buɗe ido.
Kwamishinan ya kalubalanci matasa da su zama masu ƙirƙire ƙirƙire a fannin fasaha da talla ta su ta imtanet tare da zama jakadun yawon buɗe ido na duniya daga jihar Filato.
Ya kuma shawarce su da su yi amfani da fasaha wajen samar da sabbin manhajoji da dandamali na yawon buɗe ido da za su fito da kyawun yanayi da al’adun jihar.
A jawabinsa na maraba, Babban Manajan Hukumar Yawon Bude Ido ta jihar Filato, Chuwang Pwajok, ya bayyana cewa wannan shiri yana nufin farfado da bangaren yawon buɗe ido na jihar tare da wayar da kai kan muhimmancin sa ga tattalin arzikin jama’a.
“Manufarmu ita ce gina ginshiƙin kasuwanci da ɗorewar tattalin arziki ta hanyar bai wa matasa damar samun horo da sana’a mai ɗorewa,” in ji Pwajok.
Kwamishinan ya kuma gode wa Gwamna Mutfwang bisa goyon bayansa ga shirin, ina ya yaba wa jajircewarsa wajen bunƙasa matasa da fannin yawon bude ido.
A sakonta na taya murna, Kwamishiniyar yaɗa labarai Jihar Filato, Joyce Ramnap, ta yaba da haɗin kai tsakanin Ma’aikatar Yawon Bude Ido da Hukumar yawon bude ido, tana mai cewa wannan mataki ne mai kyau wajen amfani da hazikan matasan jihar.
“Haɗa waɗannan kwararrun matasa a nan Filato alama ce ta irin damar da ke cikin mu, kuma addu’armu ita ce mu amfana da wannan haɗin kai,” in ji ta.
Ramnap ta kuma kara da cewa gwamnati na samar da yanayi mai kyau domin kasuwanci da sana’o’in hannu wajen ganin sun bunƙasa, musamman a fannoni kamar kayan sawa, sana’o’in gargajiya da sauran kayayyakin da ke nuna fasahar jihar.
Fitattun masu jawabi a wajen taron sun haɗa da Mista Eddy Enenta, Darakta a Cibiyar Kula da Horar da masu aikin Karɓar Baki da Yawon Buɗe Ido ta ƙasa dake Abuja, da Mista Victor Kuchili, babban ɗan kasuwa daga Jos, wadanda suka tattauna kan batun ‘Gina matasan Filato ta Hanyoyin Yawon Buɗe ido da Sana’oi’.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun hada da Jamima Nyako, mai shirya fina-finai da Joshua Peter Zang, mawaki da Racheal Apollos, mai shirya gasar kyau, ina suka bayyana farin cikinsu kan shirin, suna mai fatar ganin ya zama tamkar wata gada tsakanin gwamnati da matasa.
Sun ce wannan shiri zai taimaka musu wajen haɗa kai da tattaunawa da hukumomi kai tsaye, da kuma zama ginshiƙan ci gaban tattalin arzikin jihar.
Daga cikin abubuwan da suka ɗauki hankali wajen taron akwai tattaunawar kwamitin da ya kula da taron da kuma kaɗe-kaɗe da raye-raye na gargajiya.
Cikin waɗanda suka halarci wannan taro har da manyan jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa da masu kula da bangaren fasaha da masu rike da muƙaman sarauniyar kyau daga sassan jihar.