Nov 11, 2025

A cikin wannan rahoto, Samson Ebireri ya binciko yadda gashin dada ko kuma dreadlocks — wanda a da ake kallonsa a matsayin abin ƙyama — yanzu ya zama alamar ci gaba, ƙwarin gwiwa da ƙirƙirar da ake yarda da ita a tsakanin ‘yan Najeriya da ma duniya baki ɗaya. Daga shekarun baya lokacin da ake nunawa masu dada kyama zuwa cikin salon zamani, wannan gashi yana nuna banbanci a tsakanin al’umma zuwa al’umma ta fuskar haɗin kai tsakanin al’ada, bangaskiya da halayyar mutum.
Gashin dada, wanda yake da siffar murɗaɗɗen gashi da ya haɗu ko ya narke, ya wanzu tun shekaru aru-aru, kuma har yanzu yana jan hankalin maza da mata daga sassa daban-daban na duniya.
“Wannan salon gashi na musamman mutane da dama ne ke barin sa kuma ma’anarsa ta wuce kawai wani al’amari na ado,” in ji Uwargida Hoomsan, mazauniyar Abuja wadda ta koma yin dreadlocks bayan gwada wasu nau’o’in gashi daban-daban.
“Yana da arha kuma yana ɗorewa, kana yana taimaka wa gashina ya yi tsawo musamman a gaba inda ya ragu saboda ɗinke-ɗinke na shekaru,” ta ƙara da cewa.
Asalin al’ada da ma’anar ruhaniya
Gashin dada yana da zurfin tarihi da ma’anar al’ada. “An san manyan mutane irin su Samson a cikin Littafi Mai Tsarki, wanda aka ce yana da ƙarfin ban mamaki, da kuma Lord Shiva, wani ubangijin mabiya addinin Hindu wanda ake nuna shi da gashin dada,” in ji mawakiyar addinin Kirista Eve, wadda ta ce a baya an taɓa sukar ta saboda yin wannan salon dada.
Mista Ralph Zi, wanda yake mahaifi ga yara matasa, ya ce dada yana da muhimmanci a cikin al’adun Afirka, Hindu da Rastafarian. “A cikin waɗannan al’adun, galibi ana danganta dada da manyan malamai, jarumai, ko masu ruhaniya, kuma ana ɗaukar sa a matsayin alamar hikima, ƙarfin hali da ibada,” in ji shi.
Uwargida Anya Rawaya daga Jos, Jihar Filato, ta bayyana dalilinta na barin wannan salon gashi da cewa: “Ina sanye da dada saboda ya dace da ni, kuma ba kamar sauran gashi ba, yana da rahusa a wajen kula da shi. Wasu suna yinsa saboda sun karanta labaran wasu manyan mutane da suka yi shi suka zama abin koyi a zamaninsu.
“Misali, a cikin addinin Hindu, dada na Lord Shiva alama ce ta ƙarfin ruhaniya da kusanci da Ubangiji. Haka ma a cikin Rastafarianism, ana kallon dada a matsayin alamar ruhi da asalin Afirka — amma ni ina yinsa ne saboda ina son shi.”
A wasu al’adun Afirka, jarumai ne ake gani ɗauke da dada a matsayin alamar jarumtaka da ƙarfin ruhaniya. A yau, wannan salon yana ci gaba da samun karɓuwa musamman a tsakanin mawaka, masu fasaha da ƴan ƙwallo da masu fafutuka.
Uwargida Bolanle, tana tuna yarantarta, inda ta ce: “Dada yana da ma’anar ruhaniya sosai ga mutane da dama, musamman ga Yarbawa. A lokacinmu a shekarun 1970s, ana cewa kada a taɓa gashin yaran da aka haifa da dada, kuma iyayensu ba a yarda su aske shi ba sai sun yi hadaya saboda yana da ma’anar ruhaniya sosai.”
Ta ƙara da cewa, “Ni kaina dada na an yi su ne da hannu saboda ina son yadda suke sa ni in yi kyau, kuma bana kashe kudi da yawa wajen gyara su.”
Sabon salo da bayyana kai
Ga mutane da dama, dada ya zama fiye da salon gashi kawai — ya zama wata hanya ta bayyana kai. “Dada wata hanya ce ta bayyana halin mutum da salon rayuwarsa,” in ji Mama Mafeng, wata mai gyaran gashi a Rayfield dake birnin Jos.
“Ga mutane da dama, dada hanya ce ta nuna ƙirƙira da halayensu na musamman da kuma bambanta kansu daga sauran mutane.”
Ta bayyana cewa lokacin da ta lura mutane na kara son wannan salon gashi, sai ta koyi yadda ake yi da kanta — wanda ta ce “ya sa ta ci gaba da zama mai tasiri a kasuwa.”
Masu gyaran gashi, ciki har da Mama Mafeng, sun amince cewa dada yana kara samun karɓuwa na musamman a tsakanin matasa waɗanda ke ganin shi a matsayin alamar salo da ƙwarin gwiwa da kuma kyau.
Sai dai har yanzu wasu suna ganin dada a matsayin abu na daban ko mara kamala. Wasu shugabannin addini ma suna bayyana salon da cewa “ruhi ne na hauka.”
Duk da haka, kamar yadda Mista Isa Lanre ya bayyana, ya kamata mutane su fahimci ma’anarsa. “Ta hanyar fahimta da girmama ma’anar al’adar dada, za mu iya ƙara yabon salon gashi daban-daban da al’adu, musamman yanzu da samari da ‘yan mata na zamanina suka rungume shi,” in ji shi.
Ko dai saboda al’ada, ruhaniya ko kuma dalilai na ƙashin kai, babu shakka dada ya mamaye duniyar masu gyaran gashi — kuma yana sake fasalta ma’anar zama ko kuma salo, cike da kwarin gwiwa, da dogaro da kai wajen bayyana abinda mutum yake so.