Nov 8, 2025
Daga AMEDU JOSEPH, Lokoja

Farfesa na Kimiya ta Organic a Jami’ar Tarayya, Lokoja, Farfesa Olalekan Wasiu Salawu, ya bayyana damuwarsa kan halin da binciken kimiyya yake ciki a Najeriya, inda ya kira gwamnati da masu kishin kasa da su kara dagewa wajen gyara wannan yanayi.
Farfesa Salawu ya yi wannan kira ne yayin da yake gabatar da laccarsa ta 33 a jerin laccocin bude ido na jami’ar, a dandalin Adankolo da ke Lokoja kwanan nan.
A cikin laccarsa mai taken “Hidden Recipe for Life: How Tiny Complex Compounds Run the Sun”, Farfesa Salawu ya ce rashin samun damar amfani da muhimman kayan bincike ne babban cikas ga ci gaban kimiyya a Najeriya.
Ya ce kayan binciken da ake da su ba su isa ba saboda tsadar kula da su, abin da ke hana matasan masu bincike damar koyon abubuwa masu muhimmanci.
A cewarsa, “Babban dalili kuwa shi ne sakaci da ba da kudin bincike yadda ya kamata. A kasashen duniya, kudaden bincike ana rarraba su ne bisa cancanta da gasa, musamman ga ayyukan da ke da damar kawo canji mai ma’ana. Wannan tallafi yawanci daga gwamnati, kamfanonin R&D, da kuma kungiyoyin agaji yake fitowa.”
“Amma a Najeriya, jami’o’in gwamnati ne cibiyoyin binciken kimiyya na farko, kuma suna dogaro ne da tallafin gwamnati kawai wanda kuma bai wadatar ba,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Ina kira da a fara bai wa bincike na asali muhimmanci. Duk da cewa ba lallai ya kawo riba nan take ba, irin wannan bincike ne ke shimfida tushe ga sabbin abubuwa. Ku tuna da lissafi — tunanin da aka yi ƙarni da suka wuce ne ya samar da fasahar zamani da muke amfani da ita yau.”
Farfesa Salawu ya kuma soki yadda ake siyasantar da ilimi, yana mai cewa, “Yawaitar bude jami’o’in tarayya saboda tsarin rabon yankuna, ba saboda bukatar ilimi ba, ya haddasa karancin albarkatu.”
Ya tambaya, “Ta yaya za mu ci gaba da kafa sabbin jami’o’i alhali tsofaffin suna fama da sakaci?” Ya kuma jaddada cewa “idan aka karkatar da kudaden da ake kashewa wajen kafa sabbin jami’o’i don karfafa wadanda ake da su yanzu, zai fi amfani sosai ga binciken kimiyya.”
Ya kuma roki shugabanni da su “daina yin maganar kimiyya a baki kawai, su zamo masu aiwatar da ayyuka.”
Farfesan ya yaba wa kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU saboda jajircewarta, yana cewa, “Ina godiya ga ASUU. Gwagwarmayar da kuke yi ita ce ta ba mu kadan daga cikin kayan aiki da muke da su yanzu.”
Ya kuma gayyaci iyaye da su je su ga yanayin da ‘ya’yansu ke karatu, yana cewa, “Wannan gwagwarmaya ba wai tsegumi ba ne; gwagwarmaya ce domin makomar Najeriya.”
Don inganta abin gaba, ya bukaci gwamnati da ta “daina alkawuran banza, ta kuma rinka ware kudi da gaskiya da bayyani.”
Ya ba da shawarar kafa “cibiyar bincike guda daya mai na’urori na zamani a kowace yanki na siyasa,” tare da kaddamar da kudaden tallafi ga sassan kimiyya don samar da kayan aikin koyarwa da bincike.
Salawu ya jaddada cewa, “Duk wani bincike da gwamnati ke daukar nauyinsa ya zama na jama’a, a duba shi da sahihan masana, ba a boye ba. Kimiyya ba sihiri ba ce — tana bukatar gaskiya, kwazo da hadin kai.”
Ya kammala da cewa, “Lokacin canji ya yi. Mu gina tsarin binciken Najeriya da zai motsa kirkira, bunkasa ci gaba, kuma ya tabbatar da matsayarmu a idon duniya.”
Tun da farko a jawabin maraba, Shugaban Jami’ar Tarayya Lokoja, Farfesa Olayemi Akinwumi, ya bayyana jerin laccocin bude ido na jami’ar a matsayin al’ada mai daraja inda masana ke gabatar da sakamakon bincikensu ga al’umma.
Ya yaba wa Farfesa Salawu a matsayin na farko daga Sashen Kimiya da ya gabatar da irin wannan lacca, yana cewa, “Farfesa Salawu ya kafa misali nagari, wanda zai karfafa gwiwar sauran malamai su bi sahunsa.”
Ya kuma bayyana cewa taken laccar a harshen Yarbanci yana da ma’ana sosai, yana cewa, “Taken laccar ‘Èròjà ìṣèmí tó fárasín: Bí àpapọ̀ àwọn èròjà àkérèlójú (bíntìn) ṣe ń ṣíṣe ìṣèmí,’ yana nuna yadda harsunan gida za su iya bayyana ilimi cikin kwarewa. Wannan ya tabbatar da hadin kai tsakanin al’adu da kimiyya — ainihin ma’anar bincike.”