Nov 8, 2025
Daga DUMAH RANDONG, Alushi

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya yi kira ga ‘yan siyasa da su haɗa kai su yi aiki tare domin inganta rayuwar jama’a.
Mutfwang ya yi wannan kiran ne a wajen jana’izar Sanata Solomon Ewuga da aka gudanar a Mujami’ar Evangelical Reformed Church of Christ (ERCC), ta Alushi dake Jihar Nasarawa.
Jana’izar ta tara manyan mutane daga fannoni daban-daban, ciki har da gwamnonin Filato da Nasarawa da tsofaffin shugabannin al’umma da ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya da shugaban jam’iyyar APC na kasa da manyan ‘yan kasuwa tare da dangi da kuma abokan hulɗar mamacin.
A cikin huɗuba mai taken “Daga Kasa, zuwa Kasa,” Babban Sakatare na Mujami’ar Evangelical Reformed Christian Church, Rabaran Gagara Malumche, ya tunatar da masu makoki game da rashin ɗorewar rayuwa, yana mai jaddada cewa duk wata nasara ta duniya za ta kare ne a kabari.
A cikin jawabin da Mataimakiyar Gwamnan Jihar Filato, Mrs Josephine Piyo ta gabatar, Gwamna Mutfwang ya bayyana marigayin Sanata Ewuga a matsayin “dattijo na gari wanda ya rayu da sadaukarwa da kuma kishin jama’a.”
Gwamnan yaba da irin jagorancin marigayin wanda ya nuna gaskiya da hikima da jajircewa wajen kyautata rayuwar al’ummarsa.
Shi ma Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya yiwa marigayin Ewuga jinjina, inda ya bayyana shi a matsayin “ƙwararren jagora wanda ya yi aiki tukuru wajen yiwa Najeriya hidima tare da kishi da kuma tawali’u.”
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana marigayin a matsayin “Uba da mai ba da shawara,” yana mai cewa ya amfana da kwarewar Ewuga sosai.
Tsohon Ministan watsa Labarai, Labaran Maku, wanda ya yi magana a madadin tsofaffin mataimakan gwamnonin jihar Nasarawa, ya yi kira ga ‘yan siyasa da su haɗa kai inda yake gargadin cewar “akwai mutuwa da hisabi.”
Matar marigayin, Uwargida Josephine Ewuga, ta gode wa duk waɗanda suka taimaka musu lokacin rashin lafiyar mijinta da kuma bayan rasuwarsa, yayin da ta bayyana shi a matsayin “mutumin kirki mai ƙaunar jama’a.”
Daga cikin fitattun baƙin da suka karrama marigayin sun hada da tsohon Gwamnan Filato, Sanata Joshua Dariye, Basarake Aren Eggon, Mai Shari’a Ahmed Ubangari, Mishkhagham Mwaghavul, Da Hirse, da tsohon Kwamishinan yaɗa labarai na Filato, Nuhu Gagara.
Sanata Solomon Ewuga, wanda ya bar mata guda da ‘ya’ya da kuma jikoki tare da ‘yan uwa da dama, ya rasu a ranar 23 ga watan Satumbar wannan shekara ta 2025 a birnin Cairo na kasar Masar, yana da shekaru 70 da haihuwa.
