Sunday, November 9, 2025
  • Home
    • Newspaper
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • Yancin Dan Adam
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
    • Newspaper
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Yancin Dan Adam

’Yan Bindiga Sun Kashe Fasto, Sun Sace Mutane 20 a Kaduna

by The Nigeria Standard
November 8, 2025
in Yancin Dan Adam
Reading Time: 3 mins read
0 0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Nov 8, 2025

Daga JOHN FWAH, Kaduna

’Yan bindiga dauke da makamai sun kashe Fasto Rabaran Yahaya Kambasiya a unguwar Farin Dutse da ke Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna, a ranar Talata, 28 ga watan Oktobar da ta gabata, sannan suka yi awon gaba da mutane sama da ashirin.

Majalisar Mujami’ar HEKAN, wadda ake kira United Church of Christ in Nigeria (UCCN), ta bayyana da bakin cikin ta’addancin da aka yi tare mutuwar faston.

A cikin wata sanarwa da Shugaban Mujami’ar, Rabaran Amos Kiri ya fitar a Kaduna, ya la’anci wannan mummunar harin, yana mai cewa ’yan ta’adda sun kutsa kai cikin al’umma inda suka aikata ta’asa ga fararen hula marasa kariya, wanda hakan ya haifar da kisan Rabaran Kambasiya.

Rabaran Kiri ya bayyana cewa wasu mambobin HEKAN guda hudu na reshen Mujami’ar Kakude da har yanzu suna hannun masu garkuwa da su, yayin da ya bayyana cewar mambobin HEKAN, musamman a yankin Kauru, sun sha fama da hare-hare daga ’yan bindigar da ake zargin barayin shanu ne.

Ya ce, “Cikin baƙin ciki mai zurfi, a madadin ofishin HEKAN na ƙasa, ina sanar da duniya cewa wani mummunan lamari ya faru a Farin Dutse, inda ’yan bindiga suka kai hari suka kashe Fastonmu tare da sace wasu mutane.”

Kiri ya ruwaito labarin Rabaran Dauda Gambo, Shugaban HEKAN Yankin Kauru cewar ’yan bindiga ɗauke da makamai da barayin shanu sun kai hari da sassafe inda suka yi barna a cikin al’umma.

“Harin ya yi sanadiyyar mutuwar Rabaran Yahaya Kambasiya da sace mutane fiye da ashirin, ciki har da mambobin HEKAN,” in ji Kiri.

Ya kara da cewa ’yan bindigar sun shiga garin suna harbi kan mai uwa da wabi, inda suka tafka barna tare da yin awon gaba da mutanen da suka kama.

Yayin da yake karin bayani, Kiri ya ce, “Marigayi Rabaran Kambasiya da wasu sun ɓuya a gona har sai da harbin ya tsaya. Daga nan ne Rabaran Kambasiya ya fito daga maboyarsa inda aka harbe shi daga baya, harsashin ya ratsa kirjinsa, ya kuma mutu nan take.”

Shugaban HEKAN ya ce gawar faston tana dakin ajiye gawarwaki tana jiran iyalinsa su amince a binne shi, yayin da ya roki hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki su bi diddigin ’yan bindigar domin ceto mutanen da aka sace, yana mai cewa iyalan waɗanda abin ya shafa suna cikin halin baƙin ciki da tashin hankali.

Mujami’ar ta roki Allah Ya shiga tsakanin Najeriya, musamman game da taɓarɓarewar tsaro da ke ci gaba da salwantar da rayuka da barnata dukiyoyi, tare da sanya tsoro a zukatan jama’a, har ma da manoma da ke guje wa gonakinsu saboda tsoron sace su ko kuma hallaka su baki ɗaya.

“Ina rokon addu’arku ga iyalan mambobinmu da mujami’a da kuma al’umma a wannan lokaci na jarabawa,” in ji Reverend Kiri.

Idan ba’a manta ba Mujami’ar HEKAN a wannan yanki ta taɓa fuskantar irin wannan harin a ranar 4 ga watan Disambar shekarar 2024, inda aka sace mutum 50 ciki har da fasto Rabaran Francis Lawal.

Abin takaici, ɗaya daga cikin wadanda aka sace ya mutu a hannun masu garkuwa da su, yayin da wasu suka dawo da raunuka daban-daban.

Sanarwar ta kara bayyana cewa a ranar 1 ga watan Disambar bara, Bitrus Alma, yayarsa da wasu mutane biyu sun faɗa hannun masu garkuwa da mutane a  Farin Dutse, sannan a ranar 4 ga watan Janairun shekarar 2024, aka sace Rabaran Francis Lawal da wasu mutum 50.

Ko da yake ɗaya daga cikin wadanda aka sace ya mutu a hannun masu garkuwa da su, sauran sun sami ’yanci bayan wata uku inda suka dawo gida da raunuka.

HEKAN ta tabbatar da cewa ta sanar da shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN na Arewa da reshen Jihar Kaduna, da kuma Ofishin ’Yan Sanda na Kauru da sauran hukumomi da masu ruwa da tsaki sun sani.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Home
    • Newspaper
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • Yancin Dan Adam
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media