Sunday, November 9, 2025
  • Home
    • Newspaper
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • Yancin Dan Adam
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
    • Newspaper
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Yancin Dan Adam

Akume Ya Nemi Goyon Bayan ’Yan Najeriya kan Manufofin Tattalin Arzikin Tinubu

by The Nigeria Standard
November 8, 2025
in Yancin Dan Adam
Reading Time: 3 mins read
1 0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Nov8, 2025

Daga DUMAH RANDONG

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya bukaci ’yan Najeriya su mara baya ga manufofin Shugaba Bola Tinubu da ke da nufin farfado da tattalin arziki da fadada hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na kasa.

Sanata Akume ya yi wannan kira ne yayin buɗe dakin taro mai daukar mutane 250 da aka sanya masa sunan sa a Ofishin Yankin Arewa ta Tsakiya na Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta NSC dake Jos.

Sakataren ya ce tsawon shekaru Najeriya ta dogara sosai da mai da iskar gas wajen samun kuɗaɗen ta, yana mai jaddada cewa Ma’aikatar kula da bangaren sufurin jiragen ruwa ta na da damar buɗe sabbin hanyoyin arziki ta hanyar amfani da albarkatun tekun kasar.

Akume ya bayyana cewa cikin shekaru biyu da suka gabata, Ma’aikatar ta samar da sabon tsarin tafiyar da harkokin jiragen ruwa na ƙasa wadda ba ya tsaya kawai ne a kan hako albarkatun teku take ba, har da tabbatar da kula da muhallin teku don samar da damar zuba jari da ayyukan yi.

Sakataren ya yabawa Hukumar saboda jajircewar ta wajen inganta manufofin gwamnati na fadada tattalin arziki.

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, cikin jawabinsa ya yaba da aikin NSC a jihar, yana mai cewa wannan ba kawai karin ofis ba ne, amma wata dama ce ta ƙarfafa kasuwanci da jawo zuba jari da kuma samar da ayyukan yi.

Wakiliyar gwamnan, Mataimakiyar sa Ngo Josephine Piyo, ta tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da haɗa kai da NSC da sauran masu ruwa da tsaki wajen aiwatar da manufofin gwamnati kan sauƙaƙa harkokin cinikayya, sabunta hanyoyin sufuri da bunkasa fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.

Gwamnan ya kara da cewa sabon ginin da aka kaddamar zai zama alamar hadin kai da ci gaba, yayin da ya jaddada aniyarsa ta mayar da Filato cibiyar kasuwanci da masana’antu a yankin Arewa ta Tsakiya da Najeriya baki ɗaya.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana bude ɗakin taron da aka sanyawa sunan Akume a matsayin babban ci gaba da kuma amincewa da shirin ci gaba na na Shugaba Tinubu.

Wakilin Nentawe, Emma Iku wanda shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kudu, ya ce tasirin wannan aikin ya zarce samar da ayyukan yi, domin yana ƙarfafa haɗin kai na yankin da kuma samar da dandalin musayar ilimi a Arewa ta Tsakiya tare da haɗa yankin da tashoshin jiragen ruwa na ƙasa.

Ya yaba wa da Ministan dake kulada ma’aikatar, Gboyega Oyetola, da Sakatare Janar na NSC saboda jajircewarsu wajen faɗaɗa ayyukan hukumar har zuwa sassan Najeriya baki ɗaya.

Oyetola, wanda Oluwafemi Oluwatora ya wakilta, ya bayyana cewa sabon tsarin tattalin arzikin ruwa — wanda shi ne na farko a kasar — yana mayar da hankali ga hako albarkatun ruwa da kuma kiyaye su ta hanyar kare muhalli, tare da gode wa Shugaba Tinubu saboda jagorantar shirye-shiryen da ke farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Sakatare Janar na Hukumar NSC, Barista Pius Akutan, ya bayyana wannan aiki a matsayin wani babban mataki na tabbatar da rawar da hukumar ke takawa wajen inganta shirin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa na Shugaba Tinubu da kuma fadada shi.

Jawaban taya murna sun fito daga Sanata Sani Musa, Shugaban Yan majalisu da suka fito daga yankin Arewa ta Tsakiya da da Gbong Gwom Jos, Da Jacob Gyang Buba, wanda Gwom Rwei Heipang, Paul Tok ya wakilta, inda suka yaba da nasarorin Ma’aikatar da muhimmancin aikin ga yanki.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Home
    • Newspaper
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • Yancin Dan Adam
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media