Sunday, November 9, 2025
  • Home
    • Newspaper
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • Yancin Dan Adam
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
    • Newspaper
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Yancin Dan Adam

Lokacin da gurbacewa ta zama hanyar rayuwa

by The Nigeria Standard
November 8, 2025
in Yancin Dan Adam
Reading Time: 4 mins read
0 0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Nov 8, 2025

Idon Mikiya

A cikin unguwar Tudun Wada da ke Jos Birnin Jos, babban birnin Jihar Filato mai cike da cinkoson jama’a, akwai wata da ake kira Misis Bob wadda ke rayuwa tare da iyalinta a wani gidan haya mai cike da jama’a, inda iyalai guda shida ke rabon banɗaki guda ɗaya tilo da bayan gida. A ganinta, hayaniyar da ke faruwa tsakanin makwabta ita ce babbar matsalarta. Sai dai wata rana ta dawo gida ta tarar da wata injin ɗin niƙa da aka sa kai tsaye a kusa da tagar dake ɗakin barcinta.

Da farko, ta yi tsammanin makwabciyarta za ta matsar da shi daga wajen don yin aiki da shi, amma kafin wayewar gari, sautin karar niƙa mai ƙarfi da tsanani ya gallabe ta da kuma hana ta barcinta.

 “Da karfe 4:30 na safiya ne,” in ji ta cikin damuwa, “’Ya ta mai shekara biyu ta fara kuka. Ni kuma ina da juna biyu, na rikice, na firgita. Wannan ne ya zama mafarkinmu mara kyau.”

Tun daga wannan rana, iyalinta ba su sake samun nutsuwa ba. Kowane safiya kafin fitowar rana, suna matsawa zuwa falon domin tserewa daga karar da ba sa a iya jurewa. “Ba ma iya yin barci ko dan hutawa da rana — kasuwar ba ta taɓa tsayawa ba,” ta koka.

Halin da uwa ta shiga

Bayan ta haihu, Misis Bob ta lura cewa jaririnta yana kuka ba ƙaƙƙautawa duk lokacin da injin ɗin ke aiki. “Ba ya daina kuka sai an kashe injin ɗin,” in ji ta. “Daga baya na faɗa cikin damuwar haihuwa. Na fara jin takaicin jaririna.”

Ko da yake yanzu tana murmurewa, iyalinta na fuskantar barazanar korar su daga gidan muddin injin ɗin ya ci gaba da zama a wurin. Amma makwabciyarsu ta ƙi ta matsar da shi. Abin da ya kara dagula lamarin shi ne mijinta, wanda ba shi da isasshen albashi, ba zai iya barin haya ya koma wani wuri ba. “Na shiga cikin ruɗani,” ta ce cikin hawaye.

Hayaniya: Cutar da ba a lura da ita a Najeriya

Illar hayaniya — daga janareta, majami’u, kulake, har zuwa kasuwanci a gida — ta zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin muhalli da ake yi wa shiru a Najeriya. “Mun tashi da ita muka saba kamar al’ada ce,” in ji wani mazaunin Jos mai suna Milat Peters. “Ka yi korafi, sai su ce ka koma unguwa mai tsada.”

Daga magudanan ruwa da ke cike da najasa da ƙwari, zuwa makwabta da ke kiwon aladu a gefen gidajen mutane, gurbacewar muhalli a Najeriya na da fuska biyu — ana ganinta kuma ana jin ta.

Wani mazaunin Rantya, a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu, mai suna Joe Attah, ya ba da labarin yadda ya koma sabon gida, amma sai warin kiwon aladu na makwabta ya hana shi zama. “Sai da muka kai ƙara ma’aikatar muhalli kafin ta matsar da aladunta,” in ji shi.

Lokacin da tsafta ta rasa daraja

A yawancin unguwanni, rashin kyakkyawan kula da shara da sakaci da tsafta sun zama ruwan dare. Wasu suna kiwon karnuka ba tare da tsabtace muhallinsu ba; wasu kuma suna soya kifi ko sayar da rake ba tare da zubar da shara yadda ya kamata ba. Sakamakon hakan shi ne ke haifar da gurbacewar iska, ruwa da ƙasa, wanda ke cutar da lafiya da kuma lalata yanayin rayuwa.

Gurbacewar muhalli — wato zubar da abubuwa masu cutarwa ga muhalli — ba wai matsala ce ta damuwa kawai ba; ta zama babbar barazana ga lafiyar jama’a. Saboda haka, ya zama wajibi hukumomi su kafa dokoki masu tsauri game da abin da ya dace da abin da bai dace ba a cikin unguwannin jama’a.

Ya kamata injin ɗin niƙa da makamantansu su kasance a yankunan kasuwanci kawai, yayin da masana’antun da ke fitar da hayaƙi ko iskar guba su kasance nesa da gidajen jama’a. Idan ba a tsaurara doka da fadakar da jama’a ba, ‘yan Najeriya za su ci gaba da ɗaukar waɗannan haɗurra a matsayin al’ada, alhali suna lalata rayukan jama’a sannu a hankali.

Sai dai idan hukumomi basu ɗauki gurbata muhalli ta  hayaniya ko iska ko shara a matsayin lamarin da ya dace a dauki matakin gaggawa ba, ‘yan ƙasa irinsu Misis Bob za su ci gaba da wahala. Kuma babu shakka, illar hakan ga mutum da al’umma gaba ɗaya za ta kasance abin tsoro.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Home
    • Newspaper
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • Yancin Dan Adam
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media