Nuwamba 15, 2025
Daga REUTERS, JERUSALEM POST STAFF
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana fatan cewa Saudiyya za ta shiga yarjejeniyar Abraham Accords nan ba da jimawa ba.
Wannan ya fito ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a cikin jirgin Air Force One ranar Juma’a.
Trump ya ce akwai “babban sha’awa sosai” game da yarjejeniyar zaman lafiya, kuma zai tattauna wannan batu da Saudi Crown Prince Mohammed bin Salman a wani taro da za a yi a White House nan ƙarshen watan. Ana sa ran za su rattaba hannu kan yarjejeniyoyin tattalin arziki da tsaro.
Ya ce sha’awar shiga yarjejeniyar Abraham ta ƙaru tun bayan harin haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai a watan Yuni kan cibiyoyin nukiliyan Iran, wanda Trump ya bayyana da cewa: “Ya kawarda Iran daga harkar gaba ɗaya.”
Trump ya ce wannan batu zai kasance babban abin tattaunawa a lokacin taron Amurka da Saudiyya.
Lokacin da aka tambaye shi kan tattaunawar, ya ce:
“Wannan fiye da taro ne, muna girmama Saudiyya.”
Trump ya kuma bayyana cewa yana nazarin yiwuwar sayar da jiragen F-35 stealth fighter jets na kamfanin Lockheed Martin ga Saudiyya.
Ya ce: “Su na son su saya jirage da yawa. Ina duba wannan yiwuwar. Sun roƙe ni in duba. Su na son su saya F-35 da yawa – amma a gaskiya ma suna son fiye da haka, jiragen yaƙi.”
Rahoton leken asirin Pentagon da New York Times ta wallafa ranar Alhamis ya nuna damuwa cewa Sin na iya samun fasahar jiragen F-35 idan aka ci gaba da sayarwa.
